Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) da takwararta ta 'yan kasuwa, TUC, sun yanke shawar shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar Litinin mai zuwa.
Ƙungiyoyin sun cimma wannan matsaya ne bayan taron da suka yi da ɓangaren gwamnati a rabar Juma'a ya gagara haifar da ɗa mai ido.
A cewar ƙungiyoyin, sun lashi yakobin shiga yajin aiki ne sakamakon ƙememen da gwamnati ta yi na ƙin ƙara mafi ƙarancin albashi daga N60,000 da ta yi tayi, sai kima dalilin rashin janye ƙarin kuɗin wutar lantarkin da k yi.
Shugaban NLC na ƙasa, Joe Ajaero, da takwaransa na TUC, Festus Osito, babu gudu ba ja da baya game da yajin aikin.
Sun ƙara da cewa, ya zuwa ranar Litinin, 3 ga Yinin 2024 za a
fara wannan yajin aikin, kuma babu batun daktarwa har gwamnati ta cimma buƙatun NLC da TUC suka gabatar mata.
Daga cikin buƙatun nasu har da ɗaga mafi ƙarancin albashin ma'aikata zuwa N615,500, sauke farashin lantarki daga N225/kwh zuwa N65/kwh da dai sauransu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ƙungiyoyin ke tuƙuburi da shiga yajin aiki ba, wanda galibi kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu, lmarin da wasu 'yan ƙasa ke ra'ayin cewa, sun gaji da gafara sa ba su ga