Damagani ya magance matsalar shugabancin kungiyar 'yan kasuwar Keffi

Mon, 30 Dec 2024   (07:14 am) Daga   Bashir Isah
Yayin Taron Sulhu

A ranar Asabar, 28 ga Disamban 2024 shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi, Hon. Dr. Idris Ahmad Damagani, ya yi nasarar ɗinke ɓarakar da ke tsakanin shugabancin Ƙungiyar 'Yan Kasuwa reshen Keffi.

Sanarwar da shugaban tawagar yaɗa labarai na Hon. Damagani, Mubarak Musa Suleiman ya fitar ta ce, kafin wannan lokaci, shugabancin ƙungiyar ya dare gida biyu, wato tsagin Alhaji Musa Yakubu da kuma ɓangaren Alhaji Nasiru Mode wanda kowane ɓangare ke iƙirarin shi ne shugaban ƙungiyar.

Sai dai, yayin taron da suka yi a ranar Asabar da ta gabata, Hon. Damagani ya kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakanin ɓangarorin biyu ta hanyar raba muƙamai 13 da ƙungiyar ke da su a tsakanin ɓangarorin.

Ga dai yadda rabon muƙaman ya kasance:

Ɓangaren Alhaji Nasiru Mode ya samu muƙamai da suka haɗa da:

  1. Deputy Chairman
  2. Secretary
  3. Financial Secretary
  4. Organizing Secretary
  5. Auditor I
  6. PRO II
  7. Auditor II

Yayin da ɓangaren Alhaji Musa Yakubu ya tashi da muƙamai kamar haka:

  1. Chairman
  2. Treasurer
  3. Assistant Secretary
  4. Assistant Organizing Secretary
  5. PRO
  6. Woman Leader

Tun farko sai da aka bai wa ɓangarorin minti 15 a kan su sulhunta tsakaninsu wanda

a ƙarshe hakan ya ci tura. Lamarin da ya sa Shugaban Ƙaramar Hukumar da Mataimakinsa suka shiga tsakani tare da ɗaukar matakin da suke ganin ya dace.

Hon. Damagani tare da Mataimakinsa Hon. Musa Aliyu sun jaddada cewa ba za su yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da haɗin kak da zaman lafiya a faɗin ƙaramar hukumar.

Waɗanda suka halarci taron sulhun sun haɗa da Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi, Hon. Idris Ahmad Damagani da Mataimakinsa, Executive Chairman, Keffi Hon. Musa Ali; Alh. Hayatu Bawa; Alh. Muhammad Ladan (Madaki); Dan Azumi Umar da Abdullahi Ibrahim.

Sauran su ne, Alh. Yahaya Muhammad Sani; Alh. Nasiru Mode; Alh. Rabo Baba; Alh. Musa Yakubu; Alh. Husain Abin Idris; Usman Abubakar; Alhaji Sallau Umar da kuma Hon. Zulkifil Idris.