A matsayin wani mataki na soma aiki babu kama hannun yaro, Shugaban Ƙaramar Hukumar Keffi, Hon. Idris Ahmad Damagani PhD, ya yi wasu sabbin naɗe-naɗe.
Waɗanda naɗe-naɗen ya shafa sun haɗa da Hon. Ibrahim Bala Moskolo, a matsayin Sakataren Ƙaramar Hukuma; Muhammad Auwal Idris, Shugaban Ma'aikata; Alhaji Sallau Umar, Hadimi Kan Ayyuka na Musaman sai kuma Muhammad Auwal Shehu a matsayin Hadimi (PA).
Wannan mataki wata alama ce da ke nuni da sai da zaƙaƙuran mazaje Hon. Idris zai yi aiki da su domin cika ƙudurinsa na yi wa Ƙaramar Hukumar Keffi aiki
da gaskiya.
Haka nan, naɗe-naɗen na sake nuni da cewa, gwamnatinsa ta shirya kawo sauyi mai inganci a ƙaramar hukumar ta hanyar aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen da za su kyautata rayuwar al'ummar Keffi.
Da alama dai Hon. Idris ya shirya baje kolin fasaha da ƙwarewar da yake da su wajen warware matsalolin da ke yi wa Ƙaramar Hukumar Keffi dabaibayi.