AEDC na shirin datse wa sojoji, 'yan sanda lantarki saboda rashin biyan kudin wuta

Sat, 1 Jun 2024   (03:40 pm) Daga   Bashir Isah

Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya bai wa wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnati su sama da 23 wa'adin kwana uku a kan su biya bashin kuɗin wutar lantarkin da yake bin su ko kuma ya datse musu layi.

Waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da Rundunar Sojojin Najeriya da Rundunar Sojojin Saman Najeriya da Hedikwatar 'Yan Sanda da Gwamnatin Jihar Neja, ma'aikatu da sauransu.

Kamfanin ya bayyana haka ne cikin sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, kamar yadda jaridar News Point Nigeria ta

rawaito.

AEDC ya ce ya bai wa waɗanda lamarin ya shafa daga nan zuwa 3 ga watan Yuni, 2024 su biya basussukan da kamfanin ke bin su ko kuma ya datse musu lantarki.

Ya ce biyan kuɗaɗen na da muhimmanci, domin kuwa hakan zai ba shi damar ci gaba da gudanar da harkokinsa ga jama'a yadda ya kamata.