A ranar Asabar da ta gabata wasu ‘yan mata su uku suka riga mu gidan gaskiya sakamakon iftila’in ambaliyar ruwan da aka fuskanta a wasu sassan jihar Jigawa.
Bayanai daga yankin kauyen Tulla da ke Karamar Hukumar Buji a jihar sun ce, marigayan, Fatima Sule da Nasiya Sale da kuma Huwaila Sa’adu sun cimma ajalinsu ne a kan hanyarsu ta komawa gida daga gona inda ambaliyar ta yi awon gaba da su.
Jami’an tsaron Civil Defence (NSCDC) tare da hadin gwiwar mazauna kauyen suka taimaka wajen gano gawarwakin ’yan matan kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Badruddeen Tijjani Muhammad ya shaida wa manema labarai.
Rahotanni sun kuma nuna cewa, ambaliyar ta shafi jihohin Yobe da Bauchi da Kebbi inda ta lalata gidaje da gonaki masu yawa a wasu sassan jihohin.
Haka nan, iftila’in ya raba mutane da da yawa da matsugunnasu da da kuma kwashe wasu manyan hanyoyi a yankunan, lamarin da ya haifar da tsaiko na zirga-zirgar da jama’a da abubuwan hawa.
Kafin wannan lokaci, Hukumar Hasashen Yanayi ta Kasa (NiMET), ta yi hasashen za a samu aukuwar ambaliya a wasu jihhohin kasar nan sakamakon ruwan sama mai yawa
da za a fuskanta.
Don haka ne ma hukumar ta yi gargadin jihohi da dama a shiyyoyin guda shidan da aka da su za su su yi fama da ambaliya.
A cewar NiMET, jihohin da ake kyautata zaton ambaliyar za ta shafa sun hada da: Niger da Filato da Binuwai da Kaduna da Taraba da kuma Delta da Imo da Cross River da Akwa Ibom da Rivers da Bayelsa da Ekiti, sai kuma jihar Osun.
Kazalika, hasashen hukumar ya nuna za a samu matsaikaci zuwa mai yawa na ruwan sama a wasu sassan jihohin Zamfara da Kano da Borno da Gombe da Adamawa da Kogi da Kwara da Nasarawa da Ogun da Oyo da Ondo da Legas da Edo da Enugu da Ebonyi da kuma Anambra.