Rahotanni daga Jihar Kano na cewa, Majalisar Dokokin Jihar ta amince da rushe sabbin masarautu guda huɗun da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ƙirƙiro a jihar.
Majalisar ta kuma rage matsayin sarakunan masarautun da abin ya shafa zuwa hakimai.
Masarautun da lamarin ya shafa su ne; Bichi
da Gaya da Karaye da kuma Rano.
Majiyarmu ta ce an girke jami’an tsaron hukumar DSS a Fadar Sarkin Kano a safiyar Alhamis da ake soke sabbin masarautun.