Mahaifiyar Ministar Harkokin 'Yan Sanda ta kwanta dama

Thu, 27 Jun 2024   (12:20 pm) Daga   Bashir Isah
Minista Imaan

Allah Ya yi wa mahaifiyar Ministar Harkokin 'Yan Sanda, Imaan Sulaiman-Ibrahim, rasuwa.

Marigayiya Aishatu Sulaiman Danladi ta rasu ne a Abuja inda ake sa ran gabatar da jana'izarta yau Alhamis a ƙofar Fadar Sarkin Keffi da misalin ƙarfe 4:00 na rana.

Kawo yanzu, jama'a na kusa da ne na ci gaba da tururuwa don yin ta'aziyya ga ahalin marigayiyar.

Marigayiya Aishatu tsohuwar malamar makaranta ce wanda hakan ya yi tasri matuƙa wajen bai wa Imaan

kyakkyawar rayuwa.

Imaan Sulaiman-Ibrahim ita ce mace ta farko da ta fara riƙe mukamin Ministar Harkokin 'Yan Sanda a Najeriya, kuma an naɗa ta muƙamin ne a watan Yulin 2023.

Ministar ta yi fice wajen ayyukan tallafa wa al'umma wanda hakan ya sa tauraruwarta ke ci gaba da haskakawa.