Hukumar shirya jarrabawar neman gurbin karatu a manyan makarantu, JAMB, ta sanar cewar ta saki ƙarin sakamako na jarrabawar UTME na 2024 da ɗalibai suka rubuta kwanan baya.
JAMB ta ce ƙarin sakamako 531 da fitar ɓangare ne na sakamako sama da 64,000 da ta riƙe na jarrabawar UTME na bana saboda wasu dalilai.
Kawo yanzu, adadin sakamakon da hukumar ta fitar jarrabawar UTME ɗin ya kama 1,842,897.
Mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin, ya faɗa a ranar Talata cewa, hukumar na ci gaba da nazarin batun ɗaliban da ke da matsalar tantancewa kafin daga bisani ta bayyana matsayinta.
Ɓangaren sanarwar ya nuna cewa: “Kamar yadda aka yi alƙawari, hukumar ta ci gaba da tantance sakamako sama da 64,000 da aka riƙe.
“Kodayake ta saki ƙarin sakamako guda 531, wanda jimillar baki ɗaya sakamakon da aka fitar ta kama 1,842,897.”