Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Afirka, CDC a takaice, ta sanar da kafa dokar-ta-baci a kan cutar kyandar biri a matsayin barazana ga lafiyar jama’a na nahiyar.
A ranar Talata CDC ta ayyana wannan doka tana mai cewa, ya zama wajibi a dauki matakin gaggawa domin dakile cutar da kuma bai wa lafiyar al’ummomin yankin kariyar da ta dace.
Babban Daraktan CDC na Afirka, Kaseya ne ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a wani taron manema labarai da aka shirya ta intanet game da bullar cutar a Afrika.
Da yake jawabi,
jami’in ya nuna damuwarsa kan yadda cutar ke saurin yaduwa, musamman daga Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) zuwa kasashen makwabta.
A cewarsa, matakin zai taimaka matuka wajen tattara kayan aiki tare da karfafa tsarin sanarwa na kasa-da-kasa, kana matakin zai tilasta wa kasashe mambobin AU su sanar da CDC na Afirka duk matakan kiwon lafiya da aka aiwatar a cikin gaggawa.