Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dokta Mu'azu Babangida Aliyu rasuwa.
Tuni dai aka yi jana'izar Hajiya Jamila Aliyu kamar yadda Addinin Islama ya tanada a garin Minna, babban birnin jihar.
Babban limanin Minna, Malam Ibrahim Isah Fari, shi ne ya jagoranci sallar janazar a harabar babban masallacin Minna.
Waɗanda suka halarci jana'izar har da Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago da tsohon Shugaban Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar, 'yan kasuwa, sarakuna, manyan jami'an gwamnati da sauransu.
Gwamnan Neja, Umaru Bago, ya bayyana rasuwar Hajiya Jamila a matsayin babban rashi, kana ya jajanta wa iyalan marigayiyar tare da adudu'ar Allah Ya sa Aljanna makoma.