An yi kira ga matasan Jihar Nasarawa da kewaye da su kasance masu mara wa ayyukan cigaban da gwamnati ke aiwatarwa a matakai daban-daban.
Adongarin Lafia, Ibrahim Abdullahi ne ya yi wannan kira a lokacin da ƙungiyoyin matasa suka kai masa ziyarar goron sallah ranar Talata a gidansa da ke Lafia, babban birnin jihar.
Da yake yi wa matasan jawabi, Adongarin ya ce, "A matsayinmu na shugabannin gobe kuma masu ruwa da tsaki a jiharmu, mu haɗa hannu da gwamnati domin bunƙasa jiharmu ta Nasarawa. "
Ya ƙara da cewa, yana mai ƙalubalantar matasan jihar da su bai wa gwamnati cikakken haɗin kai don cimma manyan ayyukan raya
al'umma da ta sanya a gaba.
Ya ce gwamnati tana da muhimman tsare-tsaren da ta samar da nufin bunƙasa tattalin arzikin jihar da kyautata rayuwar al'umma jihar baki ɗaya.
Sai dai, ya ce gwamnati ba za ta cimma buƙatunta yadda ya kamata ba har sai ta samu haɗin kan jama'ar jihar, musamman matasa.
Daga nan, ya buƙaci matasan jihar da a haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gina jihar da bunƙasa ta ta kowane