Abba Kyari ya samu beli na mako biyu

Wed, 22 May 2024   (07:03 pm) Daga   Bashir Isah
Abba Kyari

Babbar Kotun Tarayya ta ba da belin DCP Abba Kyari na tsawon mako biyu.

Majiyarmu ta ce Kotu ta ba da belin ne don bai wa Kyari zarafin zuwa kammala jana’izar mahaifiyarsa da ta rasu.

Kazalika, Kotun ta tsayar da ranar Juma’a, 31 ga Mayu a matsayin

ranar da za ta yi matsaya kan buƙatar belin da Kyari ya gabatar mata.

Kyari na fuskantar shari’a ne kan tuhume-tuhume masu nasaba da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi daga hukumar NDLEA.