Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Jihar Imo, ta tabbatar da nasarar da Hope Uzodimma ya samua a zaɓen gwmanan jihar da aka gudanar.
Kotun ta yanke wannan hukunci ne yayin zaman shari'ar da ta yi a Abuja ranar Juma'a, 24 ga Mayu, 2024.
Kalzalika, Kotun ta yi watsi da ƙarar da Jam'iyyar Labour (LP) da ɗan takararta, Athan Achonu,
suka shigar inda suke ƙalubalantar nasarar da Uzodimma na Jam'iyyar APC ya samu a zaɓen.
Tawagar alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a, Oluyemi Akintan-Osadebay, baki ɗayan su sun amince kan cewa nasarar da Uzodimma ya samu a zaɓen halasttacciya ce.