Bayanai daga Jihar Delta sun ce, wata mata da ɗanta sun mutu bayan da suka shaƙi hayaƙin janareta a halin da suke barci.
Bayanan 'yan sandan yankin sun ce, lamarin ya faru ne bayan da marigayan suka kunna janareta daga bisani suka shigar da cikin gida kusa da ɗaki sakamakon ruwan saman da ake tare yi.
Majiyarmu ta ce, a haka waɗanda lamarin ya shafa suka yi barci, wanda a ƙarshe ba su farka ba sakamakon hayaƙi mai guba da suka shaƙa.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, SP Bright Edafe, ya ce lamarin ya faru ne kwanaki biyu da suka gabata a garin Asaba, babban birnin jihar.
Ya ƙara da cewa, 'yar matar wadda ita ma lamarin ya shafe ta, tana samun kulawar likitoci a wata asibiti da ke kusa.
Jami'in ya ce hayaƙin janareta na da matuƙar hatsari, don haka ya yi kira ga jama'a da su guji ajiye janareta a inda zai riƙa busa musu hayaƙi lokacin da yake aiki.