Sama da mutum 25 sun mutu a hatsarin mota a Oyo

Wed, 14 Aug 2024   (09:16 am) Daga   Bashir Isah
Aukuwar hatsari

Akalla mutum 25 aka rawaito sun riga mu gidan gaskiya a sakamakon mummunan hatsarin mota da ya auku ranar Talata a hanyar Ojoo-Iwo daura da yankin Agbowo/Ajao da ke Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Bayanai daga yankin sun ce, wata tirela ce mai dauke da kwanon rufin gine-gine ta yi taho-mu-gama da wasu kananan motoci da suka hada da homa bas mai daukar mutum 18 da wata taksi da kuma Honda CR-V, wanda hakan ya yi sansadiyar hasarar rayuka da dama.

Wasu da lamarin ya faru a gabansu sun bayyana cewa, matsalar birki da babbar

motar ta fuskanta hakan ya haifar da hatsarin da ya shafi sauran mototci ukun da hatsarin ya ritsa da su.

Wasu daga cikin fasinjojin da aka ceto daga hatsarin an garzaya da su asibitin da ke kusa domin yi musu magani.

Haka nan, an ga jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra da sauransu a wajen da amarin ya auku inda suka yi ta kokarin ba da